Isa ga babban shafi
India

India - An takaita zirga-zirgar motoci saboda gurbatar yanayi

Birnin New Delhi na kasar India ya haramta shigowar manyan motoci tare da sanar da takaita zirga-zirgar motoci da nufin magance yawan hayakin da ya lullube sararin samaniyar kasar da Pakistan.

New Delhi na daya daga cikin birane da suka fi fama da gurbatar yanayi.
New Delhi na daya daga cikin birane da suka fi fama da gurbatar yanayi. MONEY SHARMA / AFP
Talla

Tuni dai masana kiwon lafiya suka fara kira domin neman daukar matakan gaggawa kan lamarin, domin kauce wa illa ga lafiyar al’umma.

Kwana na uku ke nan da yankin ke fama da wannan hayaki, wanda ya turnike gari sakamakon gurbacewar yanayi wanda kuma tuni likitoci suka yi gargadin cewa matukar ba a dauki matakan gaggauwa ba, lafiyar al’ummar yankin na cikin hadari.

Daruruwan makarantu ne aka kulle a birnin na New Delhi yayin da mutane da dama suka kaurace wa zirga-zirga domin tsira da lafiyarsu.

Ministan sufuri na birnin, Kailash Gahlot, ya ce ta yin la’akari da yadda abin yake tsananta, akwai yiwuwar za a takaita zirga-zirgar kananan motoci domin a kare lafiyar al’umma.

Wani bincike ya nuna cewa kusan kowanne dare akalla manyan motocin dakon man fetur da dizel fiye da dubu hamsin ne ke ratsa birnin na New Delhi, wanda kuma ake ganin shi ne ya taka muhimmiyar rawa wajen haddasa mummunan hazon da ya gurbata muhalli.

Kungiyar likitoci ta kasar ta bukaci a samar da gyara a lamarin, yayin da a bangare guda daruruwan mutane ne yanzu haka ke kwance a asibitoci sakamakon hayakin a kasar Pakistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.