Isa ga babban shafi

"Dubban mutane zasu iya mutuwa ko wace rana a Yemen"

Wata kungiya da ke bincike kan karancin abinci a duniya, FEWS NET, ta yi gardadin mutuwar duban mutane a Yemen muddin rundunar kawance da Saudiya ke jagoranta ba ta bude manyan tashoshin jiragin ruwan kasar ba.

Wani farar hula da ke karbar magani a asibiti da ke birnin Sanaa na kasar Yemen.
Wani farar hula da ke karbar magani a asibiti da ke birnin Sanaa na kasar Yemen. REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Talla

Gargadin na zuwa ne kwana guda, bayan hukumar agaji ta Red Cross ta ce akwai mutane miliyan biyu da rabi da ke fama da rashin ruwa mai tsafta, wanda barazana ce ga fadada matsalar annobar kwalara a kasar.

Rashin bude iyakokin baban illar ce ga al’ummar Yemen, wanda shi ne hanyar da suke samu wajen shigar da kayayakin abinci, masarufi da kuma man fetur a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

A shekarar da ta gabata tsohon sakataren majalisar dinkin duniya a waccan lokacin Ban Ki-moon ya zargi Saudiya da rashin damuwa da mutuwar dubban kananan yara da kuma halin yuwar da suka fada, sakamakon yakin da take jagoranta kan mayakan Houthi na kasar Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.