Koriya ta kudu ta gabatar da tsarin tattaunawa da ta Arewa
Kasar Korea ta Kudu ta fitar da wani tsarin tattaunawar sulhu da makwabciyarta Korea ta Arewa a ranar 9 ga wannan wata na Janairu.
Wallafawa ranar:
Tattaunawar da ke biyo bayan tayin da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-Un ya gabatar a jawabansa na shiga sabuwar shekara da ke cewa, kasar na bukatar halartan gasar wasannin Olypmics da ke tafe.
Ministan hadin-kan kasar Korea ta Kudu Cho Myoung-Gyon ya fadawa taron manema labarai cewa ana sa ran tawagar kasashen biyu su zauna gaba-da-gaba domin tattaunawa.
Kasashen biyu da basa ga maciji tun kawo karshan yakin koriya a shekara ta 1950 zuwa 1953, rabonsu da zaman tattaunawa tun a cikin shekara ta 2015.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu