Isa ga babban shafi

Korea ta Arewa ta soma tattaunawa da Korea ta Kudu

Wakilan Korea ta Kudu, da ta Arewa, sun fara tattaunawa a karon farko cikin sama da shekaru biyu, bayan tsamin da dangantakarsu ta yi a baya.

Wakilan kasashen Korea ta Arewa da na Korea ta Kudu,  yayin da suka fara tattaunawa a kauyen Panmunjom da ke kan iyakar da ta raba kasashen biyu. 9 ga Janairu, 2018.
Wakilan kasashen Korea ta Arewa da na Korea ta Kudu, yayin da suka fara tattaunawa a kauyen Panmunjom da ke kan iyakar da ta raba kasashen biyu. 9 ga Janairu, 2018. Reuters
Talla

Kasashen na fatan ganin tattaunawar ta haifar da kyakkyawan sakamako, bisa ga kokarin da suke na gyara dangantakarsu da ta dade da yin tsami, tun bayan tattaunawar karshe da suka yi a shekarar 2015.

Bangarorin biyu na fatan ganin fatan ganin ci gaban ya bai wa ‘yan wasan motsa jikin Korea ta Arewa damar halartar wasannin Olympics na lokacin sanyi da Korea ta Kudu zata karbi bakunci, duk da cewa akwai ragowar zaman dar-dar tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai duk da cewa babban abinda tattaunawar ta fi karkata kai shi ne batun wasanni, kasashen duniya sun zura idanu tare da zakuwa wajen ganin yadda wannan ci gaba zai taka rawar rage zaman dar-dar a yankin na Korea, a dai dai lokacin da ake samun karuwar fargaba kan cigaba da fadada shirin mallakar makamin nukilyar Korea ta Arewa, da ya sabawa Majalisar dinkin duniya.

Shugaban tawagar Korea ta Rewa Ri Son Gwon ya ce sun fara tattaunawar tare da zuciya guda, don fatan sake samun hadin kai, yayinda shugaban tawagar Korea ta Kudu Cho Myoung-gyon ya bayyana fatan cewa yunkurin fari da kai tsaye bangarorin biyu suka yi, zai zama tamkar sun kammala shawo kan rabin yawan matsalolin da ke tsakaninsu da suke son magancewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.