Isa ga babban shafi
Iran

Amurka ta ketara iyaka - Iran

Gwamnatin Iran ta ce Amurka ta ketare iyaka, bayan daukar matakin kakabawa Shugaban sashin shari’arta, Ayatollah Sadeq Amoli-Larijani takunkumi, dan haka zata mayar da martani mai tsauri.

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani.
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani. REUTERS/Erhan Elaldi/Pool
Talla

Alwashin na Iran ya zo ne bayan da ta yi watsi da aniyar shugaban Amurka Donald Trump, na sake fasalta yarjejeniyar da ta cimma tsakaninta da kasashen turai kan shirinta na inganta makamashin nukiliya.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Trump ya bukaci sake fasalta tsarin yarjejeniyar bisa sharuddansa, bayan dage kafa wajen sake kakabawa Iran din sabbin takunkumai, da ya ce shi ne karo na karshe.

Sai dai a gefe guda, Amurkan ta kakaba sabbin takunkumai, kan wasu manyan jami’an gwamnatin kasar ta Iran 14, bisa zarginsu da cin zarafin dan adam, kan haka ne kuma ta kwace dukkanin kadarorin da suka mallaka a Amurka, tare da haramtawa ‘yan kasar gudanar da dukkan wata huldar cinikayya da jami’an.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.