"Yawan fararen hular da suka hallaka a Syria da Iraqi ya ninka a 2017"
Wata kungiya mai zaman kanta da ke sa ido kan yakin da Amurka ke jagoranta da mayakan IS a kasashen Syria da Iraqi, ta ce yawan fararen hular da rayukansu ke salwanta a dalilin yakin ya karu da kashi 200 a shekarar 2017.
Wallafawa ranar:
Kungiyar mai suna Airwars, ta ce alkalumman rayukan fararen hlar da suka salwanta, ya zarta na shekarar 2016, inda aka hallaka fararen hula tsakanin 3,923 da kuma dubu 6,102 a kasashen na Iraqi da Syria.
Kungiyar ta daganta karuwar rasa rayukan da yadda a shekarar da ta wuce, mayakan IS suka ja tunga a garuruwa ko birane masu yawan jama’a, musamman a birnin Mosul na Iraqi da kuma Raqqa da ke kasar Syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu