Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Korea ta Arewa zata maida martani kan atasayen sojin Amurka

Gwamnatin Korea ta Arewa ta yi gargadin cewa zata maida wa Amurka martanin da baza ta ji dadinsa ba, muddin ta gudanar da atasayen sojin da ta shirya yi na hadin gwiwa da Korea ta Kudu.

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un.
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un. REUTERS
Talla

A farkon watan Afrilu ma zuwa aka shirya a’a gudanar da atasayen sojin na Amurka da Korea ta Kudu, atasayen da Korea ta Arewa ke kallo a matsayin barazana gareta.

A ranar 23 ga watan fabarairu Amurka ta sanar da kakabawa wasu kamfanonin Korea ta Arewa 27 takunkumai da kuma wasu manyan jiragen ruwa 28, domin tilasta mata jingine shirinta na kera manyan makamai masu linzami, da mallakar Karin karfin makamin nukiliya.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar kara daukar sabbin matakan kakkabawa Korea ta Arewan Karin takunkuman karya tattalin arzikin, muddin wanda aka kakkaba mata a baya bayan nan bai yi tasiri ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.