Isa ga babban shafi
Afghanistan

Wani harin jiragen saman sojan Afghanistan ya hallaka yan Taliban da dalibaI masu saukar Kur'ani

Mutane da dama ne ke cike da fargaba sakamakon wani harin jiragen sama da jiragen saman sojojin Afghanistan suka kai kan wata makarantar karatun al Kur’ani dake Kunduz, arewa maso gabashin kasar, inda aka baiwa daliban takardar shaidar kammala karatu a gaban wasu shuwagabanin Taliban da dalibai da dama.

Masu binciken kasar Afghanistan  na dauke da gawar wani dan kunar bakin wake  Kabul a 9 ga maris  2018.
Masu binciken kasar Afghanistan na dauke da gawar wani dan kunar bakin wake Kabul a 9 ga maris 2018. Shah MARAI / AFP
Talla

A cewar shugaban asibitin yankin Dr Naim Mangal, mutane da dama sun rasa rayukansu a yayin da wasu sama da 15 suka jikkata, wadanda kuma suka hada da kananan yaran da aka kwantar a asibitinsa mai tarazar kilo mita 50 da lardin Dashte Archi inda harin ya wakana.

Majiyoyin tsaro da na shaidun gani da ido sun ce, fararen hula da dama ne dai suka halarci shagululanan saukar karatun kur’anin mai tsarki a lokacin da abin ya faru.

Mohammad Isqhaq wani ganau ne, ya sanar tashar TV Tolo News ta kasar Afghanistan cewa, suna cikin masalacin Akundzada inda saukar karatun ta gudana ne, wanda kuma ya samu halartar dalibai da fararen hula da yawa, da kuma wasu mambobin kungiyaryan tawayen taliban da aka gayyata ne, suka ji karar jiragen sama nan take kuma yan taliban suka tsure hankalinsu ya tashi kafin kace me tuni bamabamai sun fara sauka a ginin wannan masalaci, nan take kuma mutane da dama suka rasa rayukansu da kuma jikkata.

Wani mai daukar Hoton AFP ya ce, ya ganewa idonsa kankanan Yara da matasa da dama daga cikin wadanda suka jikkata kwakwance a kasa da kuma cikin lungunan da kwanonin asibitin

Sai dai a ta bakin kakakin ma’aikatar tsaron kasar ta Afghanistan, Mohammad Radmanish, ya musanta cewa harin ya rutsa da yara da fararen hula a masalacin, illa shugabanin Taliban a kalla su 20 da suka hada da komandansu, da aka kashe tare da jikkata wasu da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.