Isa ga babban shafi
Yemen

Kwamitin tsaron MDD zai tattauna kan sabon farmakin Saudiya a Yemen

Yau Alhamis Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da zama na musamman domin tattaunawa akan farmakin da kawancen kasashen larabawa karkashin jagorancin Saudiyya ya kaddamar, da nufin kwato yankin Hodeida daga hannun ‘yan tawayen Huthi na kasar Yemen.

Zauren Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya.
Zauren Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya. AFP
Talla

Birtaniya ce ta bukaci a yi zaman na yau, a daidai lokacin da ake nuna matukar fargaba dangane da illolin da wannan sabon farmaki zai haifar ga milyoyin mutanen kasar ta Yemen da ke rayuwa ba tare da samun daukin abinci ko kuma magunguna daga kasashen duniya ba.

Cikin wata sanarwa da ya fitar Sakataren harkokin wajen Birtaniya, Boris Johnson ya yi gargadin cewa tilas Saudiya ta kiyaye datse aikin shigar da kayayyakin abinci cikin Yemen ta tashar ruwan Hodeida.

Tashar ruwan Hodeida da a yanzu ke karkashin ikon mayakan Houthi da ke fafatawa da Saudiya, ita ce kashin bayan hanyar shigar da binci Yemen, wadda ta cikinta ake samun shigar da akalla kashi 70 na kayayyakin agaji ga al’ummar Yemen.

Sai dai a nata bangaren, Saudiya ta ce mayakan na Houthi na amfani da tashar jiragen ruwan wajen safarar makamai.

A halin da ake ciki, majalisar dinkin duniya ta ce, sama da ‘yan kasar Yemen, miliyan 22 ne ke bukatar agaji, daga ciki kuma kalla miliyan 8 na fuskantar bala’in yunwa, a dalilin yakin da ake gwabzawa tsakanin Saudiya da mayakan Houthi, tun daga shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.