Isa ga babban shafi
Isra'ila

Isra'ila ta kai hare hare a yankin Gaza

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yace dakarun kasar sun yiwa kungiyar Hamas illar da basu taba gani ba a yankin Gaza, sakamakon hari da makaman rokar da Hamas ta harba kudancin kasar.

Israila ta kai hare hare a yankin Gaza
Israila ta kai hare hare a yankin Gaza REUTERS/Ahmed Zakot
Talla

Netanyahu yace sun tattauna da ministan tsaron kasar da kuma manyan hafsoshin sojin kasar inda suka dauki aniyar kai munanan hare hare kan kungiyar Hamas.

Shima mai magana da yawun sojin, Birgediya Janar Tzvika Haimovc ya shaidawa manema labarai cewar rabon da Israila ta kai irin hare haren da ta kai yau tun yakin Gaza da akayi a shekarar 2014.

Jami’in sojin saman ya bayyana hare haren a matsayin ramako kan makaman roka kusan 100 da kungiyar Hamas ta harba kudancin Isra’ila.

Janar Haimovic yace dakarun sun yi nasarar kakkabe wasu makaman da aka harba Isra’ila, yayin da mutane 3 suka jikkata.

Ya zuwa yanzu babu cikakken bayani kan adadin mutanen da suka jikkata, sai dai wasu majiyoyi na cewa Falasdinawa 2 sun mutu a harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.