Mutane 131 sun bace sakamakon ambaliyar ruwa a Laos
Masu aikin agaji a kasar Laos na cigaba da neman mutanen da suka bace sakamakon fashewar wata madatsar ruwa wadda tayi awon gaba da mutane a cikin gidajen su.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahotanni sun ce madatsar ruwar ta fashe ne cikin dare lokacin da dubban mutane ke bacci a cikin gidajen su, abinda ya sa ruwa ya tafi da gidanjen dauke da mutane a ciki.
Ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 20, yayin da wasu 131 suka bace, kamar yadda gwamnatin kasar ta tabbatar, inda ta ce, wasu sama da 3000 kuma suka rasa muhallansu.
Shugabannin Yankin sun mika kokon barar su ga gwamnati da kungiyoyin agaji da su yiwa Allah su taimakawa mutanen su da kayan agaji da suka hada da ruwan sha da abinci da magunguna da kuma kayan sawa.
Wasu hotuna da aka wallafa sun nuna mazauna kauyukan da suka tsira da rayukan su, suna makale akan gidaje domin jiran kai musu dauki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu