Isa ga babban shafi
Syria

Mayakan IS sun sace mata da yara 36 a Syria

Wasu mayakan kungiyar IS, sun sace mata da yara kanana 36, a wani hari da suka kai kan lardin Sweida da ke yankin kudu maso yammacin kasar Syria.

Wani mayakin kungiyar IS yayin murnar kama birnin Mosul da suka yi, a ranar 23 ga watan Yuni, 2014.
Wani mayakin kungiyar IS yayin murnar kama birnin Mosul da suka yi, a ranar 23 ga watan Yuni, 2014. REUTERS/Stringer
Talla

Mutane 36 da aka sace sun hada da kananan yara 16 da kuma mata 20.

Rahotanni daga kasar ta Syria sun ce tun a ranar Larabar da ta gabata ne mayakan na IS suka kai harin, inda suka hallaka sama da mutane 250 a lardin na Sweida da kuma kauyukan da ke makwabtaka da shi.

Sai dai kakakin kungiyar Syrian Observatory da ke sa ido kan yakin Syria, Rami AbdulRahman, ya ce hudu daga cikin matan da aka sace sun kubuta, yayin da wasu biyu suka rasa rayukansu.

Kawo yanzu dai ba’a gano akalla mutane 17 da suka bace ba, yayin harin na Laraba.

Tun a shekarar 2014, kungiyar IS ta ayyana yakuna da dama daga kasashen Iraqi da Syria a matsayin sabuwar daular da ta kafa, sai dai a shekarun baya bayan nan, kungiyar ta rasa mafi rinjayen yankunan da ta kama, sakamakon murkushe karfinta da sojin Iraqi sukai, da kuma farmakin da Rasha da kuma Amurka ke jagoranta kanta a kasar Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.