Isa ga babban shafi

Girgizar kasa ta tagayyara sama da mutane 270,000 a tsibirin Lombok

Jami’an agaji a Indonesia sun ce yawan mutanen da suka hallaka a dalilin girgizar kasa mai karfin maki 6.9 da ta sake aukawa tsibirin Lombok a karo na uku, ranar Alhamis, ya kai 321.

Yankin Kayangan na arewacin tsibirin Lombok, da ke Indonesia, bayan girgizar kasar da ta afka masa a ranar 7 ga watan Agusta, 2018.
Yankin Kayangan na arewacin tsibirin Lombok, da ke Indonesia, bayan girgizar kasar da ta afka masa a ranar 7 ga watan Agusta, 2018. REUTERS/Beawiharta
Talla

Hukumar bada agajin gaggawa ta Indonesia, ta ce sama da mazauna tsibirin dubu 270, 000 sun rasa muhallansu, yayinda wasu dubu 1, 033 suka jikkata.

Kakakin hukumar agajin Sutopo Nugroho ya ce girgizar kasar ta rusa akalla kashi 3 cikin hudu na giine-ginen da ke arewacin tsibirin na Lombok.

A ranar Lahadin makon da ta gabata, Girgizar kasar mai karfin maki 7 a ma’aunin Ritcher, wadda da ta auku a yau Lahadi, ta zo ne mako guda bayan da wata makamanciyarta ta hallaka mutane 17 a tsibirin.

A shekarar 2004, wata gagarumar ambaliyar ruwa da girgizar kasa mai karfin maki 9.3 a ma’aunin Richter ta haddasa daga yankin Sumatra da ke yammacin Indonesia, ta yi sanadin salwantar akalla mutane dubu 220,000 da ke zaune a yankunan da ke gaf da tekun India, dubu 168,000 daga cikin wadanda suka hallaka ‘yan kasar Indonesia ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.