Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Afghanista ta bukaci tsagaita wuta da Taliban

Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya bukaci tsagaita wuta tsakaninsa da mayakan Taliban a dai dai lokacin da ake tunkarar bukukuwan babbar Sallah.

A cewar shugaba Ghani sai da amincewar kungiyar ta Taliban ne kudirin tsagaita wutar zai karbu.
A cewar shugaba Ghani sai da amincewar kungiyar ta Taliban ne kudirin tsagaita wutar zai karbu. @reuters
Talla

Shugaba Ghani wanda ya mika wannan bukata a wani jawabi na kai tsaye da ya yi a gidan talabijin mallakin kasar, ya ce tsagaita wutar za ta gudana ne kawai idan kungiyar ta Taliban ta amsa bukatar.

Shugaba Asharf ya ce yana bukatar tsagaita wutar ne tun daga gobe Litinin ranar Arafa har zuwa ranar haihuwar Annabi Muhammadu SAW da zai kama ranar 21 ga watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.