Isa ga babban shafi
Turkiya-Saudiya

Turkiya na bincike kan bacewar dan jarida a kasarta

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya ce yana dakon sakamakon binciken da ya bada umarnin gudanarwa, dangane da bacewar dan jarida, dan kasar Saudiya, wanda wasu majiyoyi suka ce an kashe shi bayan dan jaridar ya shiga ofishin jakadancin Saudiya dake birnin Istanbul.

Wani mai zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Saudiya, dauke da hoton dan jarida Jamal Khashoggi. (5/10/2018).
Wani mai zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Saudiya, dauke da hoton dan jarida Jamal Khashoggi. (5/10/2018). REUTERS/Osman Orsal
Talla

Tun a ranar Talatar da ta gabata ne Jamal Khashoggi, wanda yayi kaurin suna wajen sukar gidan sarautar Saudiyya da Amurka ya bace, bayanda aka bada tabbacin cewa ya shiga ofishin jakadancin Saudiya, sai dai kasar ta musanta zargin da ake mata na kashe dan jaridar.

Wata majiyar gwamnatin Turkiya ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, akwai yakinin an hallaka Jamal Khashoggi mai shekaru 59 a cikin ofishin jakadancin Saudiyya.

Sai dai, shugaban Turkiya, ya ce gwamnatinsa zata cigaba da sauraron sakamakon karshe na binciken da ake yi kan batan dan jaridar, kafin daukar mataki nag aba.

A watan Satumban shekarar 2017, Khashoggi ya tsere daga Saudiya zuwa Amurka, watanni kalilan bayanda aka zabi Muhammad Ibn Salman a matsayin mai jiran gadon sarautar Saudiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.