Cambodia
Daurin rai da rai zuwa wasu jami'an Khmer Rouge
Kotu a Cambodia ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai a kan wasu manyan jami’an tsohuwar gwamnatin kasar ta Khmer Rouge su biyu saboda samun su da laifin azaftar da jama’a lokacin mulkinsu tsakanin 1975-1979.
Wallafawa ranar:
Talla
Hukuncin da ta yanke a wannan juma’a, kotun ta samu wani mai suna Nuon Chea da lafin aikata kisan kiyashi a kan kabilar Chma musulmai tsiraru ‘yan kasar da kuma Khieu Samphan wanda ya aikata irin wannan laifi a ka ‘yan kabilar Vietnam lokacin mulkinsu.
Kungiyoyi kare dan Adam da dama ne suka gamsu da wannan hukunci da kotu ta yanke zuwa mutanen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu