Isa ga babban shafi
Indonesia

Adadin mamata dalilin aman wutar tsauni a Indonesia ya karu

Mahukuntan kasar Indonisia sun ce alkalumman mamata sakamakon igiyar ruwan tsunami da ta haddasa ambaliya, da ta samo asali daga aman wutar wani tsauni, a halin yanzu ya kai mutane 281.

Tsaunin Anak Krakatoa, daya ne daga cikin tsaunuka 127 da ke yin aman wuta lokaci zuwa lokaci a kasar Indonesia. (hoton yadda dutsen ya yi aman wuta a watan Yuli, 2018)
Tsaunin Anak Krakatoa, daya ne daga cikin tsaunuka 127 da ke yin aman wuta lokaci zuwa lokaci a kasar Indonesia. (hoton yadda dutsen ya yi aman wuta a watan Yuli, 2018) AFP
Talla

Mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa a kasar Sutopo Purwo Nugnoho, ya ce akwai wasu mutane akalla dubu daya da suka jikkata sakamakon wannan ifta’i.

Daruruwan gidaje ne suka ruguje sakamakon wannan bala’i da ya faru a kudancin tsibirin Sumatra da ke lardin Java, inda igiyar ruwa mai karfin gaske ta haddasa tumbatsar teku sakamakon aman wuta da wani tsauni ya yi.

Tsaunin dai ya share tsawon kwanaki yana aman wutar, wanda masana ke kira ‘’karamin Krakatoa’’, sai dai a ranar asabar da ta gabata lamarin ya sauya inda tsaunin ya yi aman narkakkiyar turbaya da ake iya hangowa dubban mitoci cikin sararin samaniya.

Daga nan ne fa sai aka samu motsawar igiyar ruwan tsunami, a wannan yanki da ya fi kowane samun faruwar bala’o’i a duniya.

Ko a cikin watan satumbar da ya gabata an yi mummunar girgizar kasa a tsibirin, lamarin da ya haifar da motsawar igiyar ruwan ta tsunami tare da haddasa mutuwar dubban mutane, to sai dai ba kasafai ake samun motsawar igiyar ruwa da kuma aman wuta a wannan tsauni lokaci daya kamar yadda lamarin ya faru a ranar Asabar ba.

A shekarar 2004, mummunar ambaliyar ruwa da girgizar kasa mai karfin maki 9.3 da ta afkawa yankin Sumatra da ke yammacin Indonesia, ta yi sanadin salwantar rayukan akalla mutane dubu 220 da ke zaune a yankunan kasashen gaf da tekun India, kuma dubu 168 daga cikin wadanda suka hallaka ‘yan kasar Indonesia ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.