Isa ga babban shafi
Indonesia ,India

Tauraron fina-finan kasar Indiya Kader Khan ya rasu

Tauraron masana’antar shirya fina-finan kasar Indiya ta Bollywood, Kader Khan ya rasu yana da shekaru 81, bayan shafe tsawon lokaci yana jiyya a wani asibiti da ke kasar Canada.

Jarumin fina-finan Indiya kader Khan
Jarumin fina-finan Indiya kader Khan Reuters
Talla

An haifi Kader Khan cikin shekarar 1937 a birnin Kabul na Afghanistan, mahaifinsa kuma dan kasar ta Afghanistan ne, mahaifiyarsa kuma ‘yar kasar India.

Marigayin ya soma shiga fina-finan Bollywood cikin shekarar 1973, inda ya haska a fina-finai 300 tare bada gudunmawa a wasu 250.

Wasu daga cikin fina-finan Kader Khan da suka shahara sun hada “Coolie” “Naseeb” da kuma “Aankhen” (eyes).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.