Isa ga babban shafi
China

China ta harba kumbo na farko bangaren duhun duniyar wata

China ta kafa tarihin zama kasa ta farko da ta samu nasarar harba kumbonta ‘Magpie Bridge’, wanda kuma ya sauka, a kan duniyar wata, bangaren da ba’a taba gudanar da bincike a kansa ba.Rabon da a samu irin wannan nasara, tun shekarar 1976 lokacin da kumbon Tarayyar Soviet ya yi nasarar sauka kan duniyar watan.

Wannan dai nasara ce ga shirin da China ke zubawa biliyoyin daloli na neman zama kan gaba a fagen binciken sararin samaniya.
Wannan dai nasara ce ga shirin da China ke zubawa biliyoyin daloli na neman zama kan gaba a fagen binciken sararin samaniya. Fuente: Twitter/@CGTNOfficial.
Talla

A cikin watan Disamban da ya gabata, hukumar binciken sararin samaniya ta China ta harba Kumbon binciken kimiyyan zuwa duniyar wata, wanda ya samu isa a jiya Alhamis.

Wannan dai nasara ce ga shirin da China ke zubawa biliyoyin daloli na neman zama kan gaba a fagen binciken sararin samaniya, wanda ta ke sa ran a shekarar 2022 za ta cimma burin kafa wata katafariyar cibiyar bincike a sararin samaniya nesa kadan da falakin da duniya ke kai, inda da za ta ajiye jami’anta, matakin da zai bata damar soma tura sauran jama’a zuwa kan duniyar watan.

Binciken masana dai ya tabbatar da cewa bangaren duniyar watan da Kumbon na China mai suna Magpie Bridge ya sauka, sanyinsa cikin dare ya na kai wa digiri 173 kasa da sifili, wato ya ninka santin kankara sau 173, yayinda a lokacin rana wannan bangare na duniyar wata mai ban mamaki, zafinsa yake ninka na tafasasshen ruwa sau 173.

Masana sun kuma kiyasta cewa, kwana guda akan duniyar watan dai dai ya ke da tsawon kwanaki 14 a duniyar da mu ke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.