Isa ga babban shafi
Turkiya-China

Erdogan ya nemi China ta kulle sansanin azabtar da musulmin Uighur

Turkiya ta bukaci China ta rufe sansanonin da ta ke tsare mabiya addinin Islama daga kabilar Uighur sakamakon mutuwar wani fitaccen mawaki Abdurehim Heyit.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan Reuters/路透社
Talla

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Turkiya ta gabatar ya ce mawakin da aka daure shekaru 8 a gidan yari ya mutu sakamakon azabtarwar da ake musu a irin wannan sansani.

Su dai 'yan kabilar Uighur su ne tsiraru kuma mabiya addinin Islama a kasar ta China wadanda ke zaune a yankin Xinjiang, kuma harshen su ya so ya yi kama da na Turkiya.

China ta bayyana bukatar Turkiyar a matsayin abinda ba zata amince da shi ba.

Ko a baya-bayan nan dai daruruwan 'yan Kabilar ta Uighur sun yi ta yin hijira zuwa Turkiya don samun saukin rayuwa daga azabtarwar da su ke fuskanta can a China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.