Isa ga babban shafi
India

Mutane miliyan 900 na kada kuri'u a zaben India

Kimanin mutane miliyan 900 ke kada kuri’u a zaben gama-gari a India, zaben da ake kallo a matsayin mafi girma a duniyar demokradiya. Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa, akwai yiwuwar Jam’iyyar hadaka ta Firaministar kasar, Nerandra Modi ta samu nasara a zaben.

Wasu daga cikin masu kada kuri'u a India
Wasu daga cikin masu kada kuri'u a India REUTERS/Ahmad Masood
Talla

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa, jam’iyyar hadaka mai mulkin kasar za ta samu karamin rinjaye a zaben saboda yadda ta mayar da hankalinta kan batutuwan da suka shafi tsaro da samar da ayyuka da kuma tallafawa kananan manoma.

Kodayake alkaluma sun nuna cewa, matsalar rashin aikin yi ta ta’azzara a mulkin Nerandra Modi, in da a cikin watan Fabairun da ya gabata, aka samu karuwar marasa aiki da kashi 7.2.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ta kuma nuna cewa, Mr. Modi ya kara samun tagomashi a idan Indiyawa saboda tsayin-dakarsa wajen mayar da martani kan harin da ya kashe sojin kasar 40 a Pakistan, lamarin da ya tilasta wa gwamnatin Modi kaddamar da hare-heren sama a karon farko tun shekarar 1971 a Pakistan.

Sai dai ana zargin Modi da nuna wa Musulman kasar miliyan 200 banbanci, saboda yadda yake fifita mabiya addinin Hindu masu rinjaye.

Babban mai adawa da Modi na jam’iyyar Bharatiya Janata a wannan zabe, shi ne Rahul Gandhi na jam’iyyar Congress, kuma za a shafe kimanin wata guda kafin kammala zaben baki daya, yayinda za a sanar da sakamakon karshe a ranar 23 ga watan Mayu mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.