Isa ga babban shafi
Sri Lanka

Sri Lanka ta haramta wasu kungiyoyin addini 2 bayan harin Easter

Shugaban kasar Srilanka, Maithripala Sirisena ya haramta wasu kungiyoyin addini biyu na National Thawheed Jammath wato NTJ, da kuma Jamathei Millathu Ibraheem wato JMI wadanda ake zargi da hannu a hare-haren ranar Lahadin da ta gabata wanda ya hallaka mutane kusan 300.

Shugaban kasar Sri Lanka Maithripala Sirisena tare da Firaminista Ranil Wickremesinghe
Shugaban kasar Sri Lanka Maithripala Sirisena tare da Firaminista Ranil Wickremesinghe ©REUTERS/Dinuka Liyanawatte
Talla

Cikin sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar, ta ce shugaba Sirisena ya yi amfani da karfin ikon kujerarsa wajen haramta kungiyoyin guda biyu, wanda kuma ya ce haramcin zai fara aiki daga ranar Talata.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar, Dharmasri Ekanayake ya ce matakin zai bai wa gwamnati damar karbe iko da duk wani abu da ya ke mallakin kungiyoyin biyu.

A litinin din da ta gabata ne, wasu rahotanni suka sanar da cewa, Jagoran kungiyar ta NTJ na cikin wadanda suka suka yi kunar bakin wake a makon na jiya.

A cewar gwamnatin kasar ta Sri Lanka, ba su dauki matakin dakatar da kungiyoyin biyu ba har sai da suka samu kwararan hujjojin da za su gamsar da ‘yan kasar da su.

Kawo yanzu dai, jami’an ‘yan sandan Sri Lanka sun kame fiye da mutane 100 da ake zargi da kai hare-haren ciki kuwa har da ‘yan kasashen Masar da Syria

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.