Isra'ila da Falasdinawa sun dakatar da kaiwa juna farmaki
Shugabannin Falasdinawa sun amince da shirin tsagaita wuta da Israila da safiyar yau Litinin, bayan jerin kazaman hare-haren da bangarorin biyu suka rika kaiwa juna, wadanda suka yi sanadiyar rasa rayuka.
Wallafawa ranar:
Kasar Masar ce ta jagoranci tattaunawar tsagaita wutar da aka kulla da misalin karfe 4.30 na asubahin yau, kamar yadda jami’an kungiyar Hamas da na Islamic Jihad suka bayyana.
Zuwa yanzu hukumomin Israila basu ce komai ba kan yarjejeniyar, sai dai rahotanni sun ce an dakatar da kai hare hare daga kowanne bangare.
Wissam Zoghbar, wani jami’in kungiyar Falsdinu yace cikin yarjejeniyar tsagaita wutar harda sakin mara ga hanyoyin shiga Gaza da wuraren kamun kifin Falasdinawa da kuma inganta samar da wutar lantarkin Yankin.
Akalla Falasdinawa 23 aka kashe a fafatawar, yayin da aka kashe Yahudawa 4.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu