Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta yi watsi da tayin tattaunawar sulhu da Amurka

Iran ta yi watsi da tayin shiga tattaunar sulhu da Amurka kan yarjejeniyar nukiliyarta, muddin bata janye takunkuman da ta kakaba mata ba.

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani.
Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani. AFP / Sabah Arar
Talla

Kasar ta Iran ta bayyana haka ne, sa’o’i kalilan bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce a shirye suke, su tattauna da Iran, amma ba tare da gindaya wasu sharudda ba.

A ranar Lahadi Mike Pompeo ya ce a shirye Amurka take ta tattauna da Iran kan yarjejeniyar nukiliyar kasar, to amma ba tare da sharadin janye takunkuman karya tattalin arzikin da aka kakaba mata ba.

Karo na farko kenan da gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump ta gabatar da tayin tattaunawar sulhu da Iran, tun bayan tsamin da dagantakarsu ta yi, sakamakon janye Amurkan da Trump yayi daga cikin yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya a shekarar 2015.

Kalaman na Pompeo dai martani ne kan jawabin shugaban Iran Hassan Rohani na ranar asabar, wanda ya jaddada cewa, ba za su lamunci fuskantar cin zali da kuntatawa don tilasta musu shiga tattaunawa da Amurka ba.

Tuni dai Iran ta hannun kakakin ma’aikatar wajenta Abbas Mousavvi, ta ce tilas Amurka ta sauya matsayarta kan takunkumai da sauran matakan kuntatawar da ta kakaba mata, muddin da gaske gwamnatin Trump din take yi kan tayin tattaunawar sulhun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.