Isa ga babban shafi

Fiye da mutane dubu 400 sun tsere daga Syria cikin watanni 3- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa fiye da mutane dubu 400 ne suka fice daga kasar Syria cikin watanni 3 bayan da gwamnati ta daura damarar kakkabe ‘yan tawayen da ke rike da yankin Idlib.

Wani sansanin 'yan gudun hijira da rikici ya koro su daga Syria
Wani sansanin 'yan gudun hijira da rikici ya koro su daga Syria REUTERS/Ali Hashisho/File Photo/File Photo/File Photo
Talla

Babbar jami’ar hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Michelle Bachelet wadda ta nuna damuwa kan yawaitar rasa rayukan fararen hular da ake fuskanta a Syrian cikinw atannin baya-bayan nan, ta ce akwai damuwa game da yadda hare-haren ba sa waigi kan Makarantu Asibitoci da kuma kasuwannin yankin.

A cewar Bachelet wannan ne mafi tsanantar lokacin da hare-haren sojin gwamnati yafi shafar fararen hular da basu ji ba basu gani ba, a yankin na Idlib wanda ke matsayin na karshe da ke hannun bangaren adawa.

Majalisar Dinkin Duniyar ta bayyana cewa Gwamnatin Syria da babbar abokiyarta Rasha sun gaza mutunta yarjejeniyar kare raukan fararen hular da ke yankin da aka cimma da kasashen duniya bara.

Majalisar ta bayyana cewa tun cikin watan Aprilu Rasha ke jagorantar hare-hare kan yankin ba kuma tare da kebe makarantu kasuwanni ko kuma asibitoci dama sauran wuraren taruwar jama’a, dalilin da ya haddasa asarar rayukan akalla farar hula dubu 740.

A cewar David Swanson jami’in hukumar agaji ta majalisar dinkin duniya da ke kula da rikicin na Syria, daga watan Aprilun zuwa yanzu fiye da mutane dubu 400 sun fice daga kasar zuwa makota.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.