Isa ga babban shafi

Zanga-zangar kyamar gwamnati na ci gaba da tsananta a Hong Kong

Dubban jama’a galibi matasa a Hong Kong sun ci gaba da gangamin adawa da gwamnatin yankin mai ra’ayin China, a mako na 8 da fara zanga-zanga tun bayan kudirin dokar da ya bukaci fara aikewa da masu laifi China don fuskantar hukunci.

Tururuwar masu zanga-zanga a yau Asabar
Tururuwar masu zanga-zanga a yau Asabar @Reuters
Talla

Duk da kamen jama’ar da ake ci gaba da yi baya ga jikkata wasu da dama a makon jiya, rahotanni sun bayyana cewa adadin masu zanga-zangar ya karu a wannan karon.

A wannan makon ma, masu zanga-zangar sun fito ne da fuskarsu a rufe, sun rike janye shingayen kan titina tare da rufde babbar hanyar da za ta sada su yankin Tsim Sha Tsui matakin da ya haddasa cunkoson ababen hawa tare da hana jami’an tsaro ka iwa garesu.

Dubban masu zanga-zangar dai na neman murabus din shugabar yankin na Hong Kong tun bayan bore kan dokar da ta juye zuwa zanga-zangar kin jinin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.