Isa ga babban shafi

Taliban ta sha alwashin katse hulda da kungiyoyin ta'addanci

Kungiyar Taliban da ke kasar Afghanistan ta sanar da warware matsalar da ke tsakanin ta da Amurka dangane da abinda ya shafi lokacin da dakarun ta za su fice daga cikin kasar, yayinda ita kuma Taliban za ta katse hulda da duk wata kungiyar Yan ta’adda.

Shugaban sashen siyasar kungiyar Taliban Mohammad Abbas Stanakzai
Shugaban sashen siyasar kungiyar Taliban Mohammad Abbas Stanakzai REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Kungiyar Taliban da ke jerin tattaunawa da wakilan gwamnatin Amurka ta sanar da wannan cigaba da aka samu, yayin ganawar da suka yi a Qatar, yayin da Jakadan Amurka dake jagorancin taron Zalmay Khaliad yace an samu gagarumar cigaba a wajen taron.

Bangarorin biyu sun kwashe kwanaki biyu su na ganawa a tsakaninsu, yayinda kwararru daga bangarorin ke bada shawara kan irin matakan da suka dace a dauka.

Khalizad da ke jagorancin yunkurin kulla yarjejeniyar zaman lafiya domin kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 18 ana fafatawa a kasar, ya sanya shirin tsagaita wuta da kuma tattaunawa a matsayin manyan kudirorin da ke gaban sa, duk da adawar da Taliban ke yi na ganawa da jami’an gwamnatin Afghanistan, wadanda suka bayyana su a matsayin karen farautar Amurka.

Sai dai duk da tattaunawar da ke gudana, kungiyar Taliban na cigaba da kai munanan hare hare da kuma barazana ga zaben shugaban kasar da za’ayi ranar 28 ga watan Satumba.

Jakadan Amurka Khalizad ya bayyana aniyar san a ganin an kulla yarjejeniyar zaman lafiya nan da ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa, domin bude kofar janyewar sojojin Amurka da na kungiyar NATO 20,000 daga kasar ta Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.