Isa ga babban shafi
Hong Kong

An gudanar da zanga-zanga kashi biyu a Hong Kong

Masu fafutukar kafuwar mulkin dimokaradiya irin na Turai a Hong Kong sun sake kaddamar da gagarumar zanga-zanga yau asabar, bayan ta makon jiya da ta gurgunta filin jiragen saman yankin, matakin da China ta kamanta da ta’addanci, tare da aikewa da dakarun kan iyakarta da yankin na Hong Kong.

Wasu masu zanga-zanga a Hong Kong.
Wasu masu zanga-zanga a Hong Kong. Reuters/Kim Hong-Ji
Talla

Sabuwar zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da dubban masu goyon bayan gwamnatin ta Hong Kong da kuma China ke gudanar da nasu gangamin, inda suke yin Ala-wadai da takwarorinsu, tare da marawa ‘yan sanda baya.

Tagwayen zanga-zangar dake gudana a Hong Kong ya nuna yadda ake ci gaba da samun rarrabuwar kai a yankin, tun bayan barkewar, zanga-zangar da ta soma kan adawa da kudurin dokar mika masu laifi daga yankin zuwa China don fuskantar hukunci, da yanzu ta rikide zuwa neman karin kwarya-kwaryar ‘yancin yankin daga kasar ta China.

A gefe guda kuma kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci tattaunawar sulhu don kwantar da hankula a yankin na Hong Kong, inda aka shafe sama da makwanni goma ana zanga-zangar adawa da gwamnati, la’akari da yadda a kusan kowane lokacin ake yin arrangama tsakanin masu zanga-zangar, da jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.