Isa ga babban shafi
Asiya

Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin India da Kashemir

Firaministan Pakistan Imran Khan ya jagoranci wani gangami da ya hada dubun dubatan al’ummar kasar wadanda suka fito kwansu da kwarkwatarsu don gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna adawa da ayyukan gwamnatin India a Kashmir a dai dai lokacin da kasashen biyu masu makamin nukiliya ke ci gaba da nunawa juna yatsa.

Firamininstan Pakistan Imran Khan
Firamininstan Pakistan Imran Khan REUTERS/Stringer
Talla

Zanga-zangar ta yau ta hada duban mutanen yankin da suka fito domin nuna rashin amincewar su,an jin jiniyar motocin tsaro da kuma wake na taken kasar Pakistan da kashmir da ke tashi , yayin da aka tsayar da harkokin zirga-zirga na wasu mintina don nuna goyan baya ga zanga-zangar

A babban birnin kasar Islamabad ne dandazon mutane suka hallara a gaban ginin ofishin gwamnatin kasar, inda firaministan Imran khan ya yi wa al’ummarsa jawabi tare da daukar alwashin cigaba da taya kashmir yaki har sai an kawo karshen rikicin domin yantar da yankin Himalaya

Tashin hankula dai na dade zafi tsakanin kasashe biyu masu makamin nukiliya, sakamakon umarnin da shugaba Modi na India ya bayar na kwace ikon cin gashin kai na wani yankin kasar dake kashmir zuwa karkashin ikon gwamnatin Delhi

A na cikin makonni hudu da yanke duk wata kafar sadarwa da kuma daukar tsatsaura matakan hana zirga zirga a yankin.

Wannan zanga zangar dai itace ta farko kafin a fara irinta a duk mako a kasar har sai shugaba khan ya kai ziyara birnin New york na Amurka don hallartar babban taron majalisar dinkin Duniya .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.