Isa ga babban shafi
Afghanistan

Masu kada kuri'a sun bijirewa barazanar Taliban

Al’ummar Afghanistan na ci gaba da kada kuri’a a zaben shugabancin kasar yau asabar, duk da barzanar kai hare-haren da mayakan Taliban suka yi, inda jim kadan bayan soma zaben wani harin bam ya jikkata mutane 15 a wata rumfar zabe dake birnin Kandahar.

Wasu mata dake shirin kada kuri'a a zaben shugabancin Afghanistan.
Wasu mata dake shirin kada kuri'a a zaben shugabancin Afghanistan. Reuters
Talla

Harin dai ya zo ne awanni kalilan bayan soma kada kuri’a a zaben shugaban kasa, cikin tsauraran matakan tsaro.

‘Yan takara 14 ne ke fafatawa a zaben shugabancin na Afghanistan, sai dai hamayyar tafi zafi tsakanin shugaba mai ci Ashraf Ghani da tsohon mataimakinsa Abdullah Abdullah.

Akalla jami’an tsaron Afghanistan dubu 100 gami da taimakon jiragen yakin Amurka ke aikin sintiri don tabbatar da tsaro yayin zaben na yau, inda ake kada kuri’a a rumfunan zabe dubu 5000 a sassan kasar.

A ranar Juma'a hukumomin tsaron Afghanistan suka haramta zirga-zirga, da kuma shigar manyan motoci cikin babban birnin kasar Kabul, domin dakile duk wani yunkuri na kai hare-haren kunar bakin wake, kafin ko kuma a lokacin zaben shugabancin kasar dake gudana a yau asabar.

A baya bayan nan, Taliban da ta kai munanan hare-haren kunar bakin wake, kan tarukan siyasa da ofisoshin jam’iyyu, ta gargadi mutane da cewa su kauracewa fita kada kuri’a a zaben na wannan asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.