Isa ga babban shafi
Gambia-Myanmar

Suu Kyi za ta jagoranci masu kare Myanmar kan tuhumar cin zarafin 'yan Rohingya

Jagorar Myammar, wacce ta taba lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel, Aung San Suu Kyi za ta jagoranci wata tawaga zuwa kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya don kare zargin da ake wa kasar na kisan kare – dangi kan al’ummar Musulmi ‘yan Rohingya.

Aung San Suu Kyi, jagorar Myanmar
Aung San Suu Kyi, jagorar Myanmar Pierre Emmanuel Deletree/Pool via REUTERS
Talla

Kasar Gambia ce ta shigar da wannan kara a kotun hukunta manyan laifuka a madadin kasashe 57 da ke kungiyar hadin kan Musulmi.

A cikin korafin da aka shigar, an zargi Myanmar da laifin bijirewa muradin taron Majalisar Dinkin Duniya na 1948, da ya yi hani da kisan – kare- dangi, ta wajen diran mikiya da sojojin kasar suka yi wa al’ummar Rohingya a jihar Rakhine a shekarar 2017.

Yayin sauraron karar a karon farko, ana sa ran kasar Gambia, wacce Musulmi suka fi rinjaye a cikinta, ta bukaci kotun ta bijiro da wata doka da za ta kare ‘yan Rohingya, gabanin daukar matakin ci gaba da shari’ar gaba daya.

Ofisin Suu Kyi, a wata sanarwa ya ce da kanta za ta wakilci tawagar da za ta kare mutuncin kasar Myanmar, kuma akwai fitattun lauyoyi da suka lakanci aikinsu a tawagar.

Kasarta ci gaba da kare matakin sojin da ta dauka kan Musulmi ‘yan Rohingya, inda ta zake cewa ta yi ne don kawar da ‘yan ta’adda a yankin, tana mai cewa kwamitocin ta ma sun wadatar wajen gudanar da binciken zargin aikata ba daidai ba.

‘Yan Rohingya dubu 740,000 aka tilasta wa arcewa daga gidajensu a shekarar 2017 zuwa sansanoni a Bangladesh, bayan mummunan matakin da soji ta dauka a kansu, abin da masu binciken Majalisar Dinkin Duniya suka kira kisan –kare – dangi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.