Isa ga babban shafi
India

Majalisar India ta amince da dokar hana Musulmi zama dan kasa

Majalisar dokokin India ta amince da kudirin dokar nan da ta ba da damar zama dan kasa ga bakin haure daga wasu kasashen ketare wadanda ba musulmai ba, yayin da gwamnatin kasar ta girke daruruwan dakaru a arewa maso gabashin kasar inda mummunar tarzoma ta tashi saboda wannan doka.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da dokar hana Musulmi zama dan kasa a India
Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da dokar hana Musulmi zama dan kasa a India JEWEL SAMAD / AFP
Talla

Wannan kudirin doka zai bai wa gwamantin India damar bada takardar zama dan kasa ga miliyoyin bakin-haure da suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba daga kasashe 3 da ke makwabtaka da ita, gabanin shekarar 2015, muddin su ba muslmai ba ne.

Kudirin ya samu goyon bayan ‘yan majalisar dattawar kasar 125, yayin da 105  suka nuna akasin haka, bayan majalisar wakilai ta amince da kudirin.

Za a kuma aike da shi zuwa ga shugaban kasa don sanya hannu tare da hatimcewa.

Masu adawa da wannan kudiri sun yi barazanar garzayawa kotun koli don kalubalantar sa, inda suka ce ya yi hannun riga da shikashikan daidaito da  fifita wani addini bayan kundin tsarin mulkin kasar ya haramta haka.

Kungiyoyin Musulmai da  ‘yan adawa da masu rajin kare hakkin bil'adama na kallon wannan mataki a matsayin shirin Firaminista Narendra Modi na danne Musulmai miliyan 200 da ke kasar, zargin da tuni ya musanta.

Wannan batu ya janyo zanga–zanga a jihohin arewa maso gabashin kasar, inda mazauna wurin ke adawa da yadda ‘yan Hindu ke kwarara zuwa kasar daga Bangladesh da ke makwabtaka da India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.