Isa ga babban shafi
Japan-Lebanon

Carlos Ghosn ya tsere Lebanon daga hannun mahukuntan Japan

Gwamnatin Faransa ta nuna matukar mamaki da kubucewar tsohon shugaban kamfanin Nissan Carlos Ghosn daga hannun hukumomin Japan wata guda gabanin fara sauraron shari’arsa kan badakalar kudaden kamfani, inda kuma zai iya fuskantar hukuncin kisa ko kuma daurin rai da rai a gidan yari.

Tsohon shugaban kamfanin Nissan Carlos Ghosn.
Tsohon shugaban kamfanin Nissan Carlos Ghosn. REUTERS/Issei Kato
Talla

Carlos Ghosn wanda ke da fasfuna kasashen Faransa Lebanon da kuma Brazil tun cikin daren jiya Litinin ya yi batan dabo a Japan yayinda jami’an tsaron shige da fice suka gaza gano sawunsa da kuma inda nufa gabanin gano shi a Lebanon tun da safiyar yau Talata.

Masana tsaro dai na ci gaba da diga ayar tambaya kan yadda mai laifin Ghosn ya iya tserewa daga kasar duk da matakan tsaron da aka gindaya masa, inda ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta bayyana cewa abin mamaki ne matuka yadda Ghosn ya iya tserewa daga Japan ba tare da an iya gano shi a filin jirgi ba, ko da dai wata majiya ta bayyana cewa mai laifin ya yi amfani da wani suna na daban don tserewa daga kasar.

A cewar ma’aikatar ta Faransa Ghosn wanda sharadin belinsa da mahukuntan Japan suka bashi bai sahale masa barin kasar ta kowacce fuska ba, ya zama wajibi ya karbi hukunci kan laifin da ya aikata.

A cewar Taichiro Motoe dan majalisa daga jam’iyya mai mulki ta LDP tserewar da Ghosn ya yi baban laifi ne da zai janyo masa karin tsattsauran hukunci, yayin da Mashisa Sato na jam’iyyar adawa ta LDP ke cewa babu yarjejeniyar bayar da mafaka tsakanin Japan da Lebanon a don haka dole ne Ghosn ya dawo don fuskantar hukunci kan laifin da ya aikata.

Sai dai Ghosn mai shekaru 65 wanda ya jima yana kalubalantar tsarin shari’ar Japan ya ce bai kaucewa shari’a ba, kawai dai ya tsere Japan ne don kaucewa rashin adalcin da za a iya yi masa a Japan

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.