Isa ga babban shafi
Afghanistan

'Yan adawa za su kafa gwamnati a Afghanistan

Bayan shafe tsawon watanni ana dakon fitar da sakamako, Hukumar Zaben Afghanistan ta ayyana shugaba Ashraf Ghani a matsayin wanda ya sake lashe zaben kasar, amma babban abokin hamayyarsa Abdullah Abdullah ya kalubalancin sakamakon, yana mai barazanar kafa gwamnatinsa ta daban. Hukumar Zaben ta ce, Ghani ya samu kashi 50.64, yayin da Abdullah ya samu kashi 39.52.

Madugun 'yan adawar Afghanistan Abdullah Abdullah
Madugun 'yan adawar Afghanistan Abdullah Abdullah REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Sakamakon zaben na ranar 28 ga watan Satumban bara na zuwa ne bayan jinkirin da aka samu saboda zarge-zargen tafka magudi da bangaren adawa ya yi, lamarin da ya sa aka sake kida kuri’u.

Sai dai Abdullah Abdullah da ya kasance babban mai hamayya da shugaba Ashraf Ghani, ya hakikance cewa, su suka yi nasara.

Yanzu haka aniyarsa ta yunkurin kafa gwamnatinsa ta daban, ta sa an tuna abin da ya faru a zaben shekarar 2014, lokacin da Abdullah din ya yi bore bayan an ayyana Ghani a matsayin wanda ya yi nasara.

A wancan lokacin dai, magoya bayan Abdullah sun gudanar da zanga-zanga kafin Amurka ta tsoma baki da zummar jagorantar cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai a halin yanzu, Amurka ba ta da cikakkiyar sha’awa a siyasar Afghanistan kamar yadda ta nuna a 2014 a zamanin mulkin Barack Obama. Hasali ma kokari take ta cimma yarjejeniya da mayakan Taliban domin janye dakarunta.

Ita ma kungiyar Taliban ta yi watsi da nasarar da aka ce shugaba Ghani ya sake samu a wannan karo, nasarar da ta bayyana matsayin haramtacciya wadda kuma za ta yi cikas ga yunkurin samar da zaman lafiya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.