Isa ga babban shafi
WHO-Corona

Coronavirus na yaduwa zuwa wasu kasashe

Hankula sun tashi a yau Asabar sakamakon sanarwar samun karuwar wadanda suka kamu da cutar coronavirus a wajen kasar China, yayin da hukuimar lafiya ta Duniya ke kashedin cewa fatar dakile na dada kulewa.

Sojojin ruwa na Koriya ta Kudu yayin da suke sa shinge a hanya saboda zuwan wadanda ake zargin sun harbu da coronavirus
Sojojin ruwa na Koriya ta Kudu yayin da suke sa shinge a hanya saboda zuwan wadanda ake zargin sun harbu da coronavirus Yonhap/Handout via REUTERS
Talla

Kashedin na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na zuwa ne bayan an samu bature na farko da ya mutu bayan ya harbu da cutar ta COVID 19, wacce ta fara bulla a watan Disamban shekarar data gabata, kuma yanzu ta bazu zuwa kasashe sama da 25, kuma yanzu haka fiye da mutane 12 sun mutu a wajen China.

Wani dan Italiya, mai shekaru 78 ya mutu bayan an gano ya harbu da cutar, yayin da a Iran, wadanda suka mutu sun kai 4, wasu kuma sun kamu a Lebanon da Isra’ila.

Hukumomi a Koriya ta Kudu sun sanar da mutum na biyu da ya mutu sakamakon cutar, tare da karuwar masu kamuwa a Asabar dinnan.

Italiya ta rufe garuruwa 10, kana ta tilasta wa mutane dubu 50 ci gaba da kasancewa a gida babu fita, mataki mai kama da wadda China ta dauka, inda ta rufe birane a lardin Hubei.

A China, ana samun raguwar sabbin masu kamuwa da cutar a wajen lardin Hubei, inda aka killace miliyoyin mutane.

A Asabar dinnan, mutane 31 ne kawai aka sanar sun harbu da cutar, yayin da adadin wadanda suka kamu a kasar ya zarce dubu 76.

Wannan cuta ta yi sanadin mutuwar mutane 2,345 a China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.