Turkiya-Syria
Turkiya ta rasa dakarun ta 33 a Syria
Gwamnan jihar Hatay a Turkiya dake iyaka da Syria Rahmi Dogan ya ce akalla dakarun kasar Turkiyan 33 ne suka halaka yayin wani farmakin jiragen yaki, da ake kyautata zaton sojin Syria ne suka kai a lardin Idlib.
Wallafawa ranar:
Talla
Asarar rayukan gwamman sojin na Turkiya dai na zuwa makwanni bayan tsamin da dangantakarsu ta yi da Rasha kan farmakin da sojin Syrian ke kaiwa ‘yan tawaye a Lardin na Idlib dake zaman tungar karshe a garesu.
Tuni dai majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewar barazanar kazancewar sabon yaki a Syria na karuwa a duk bayan sa’a 1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu