Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta kai hari kan dakarun gwamnatin Afghanistan

Kungiyar Taliban da ke Afghanistan ta kaddamar da hari kan sansanin sojin gwamnati, sa’oi bayan kawo karshen takaita bude wutar da ta yi, matakin da ake ganin zai rusa yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kulla da kasar Amurka.

Wasu daga cikin jagororin Taliban
Wasu daga cikin jagororin Taliban KARIM JAAFAR / AFP
Talla

Wani jami’in Ma’aikatar Tsaron Kasar ya ce, Taliban ta kai hare-hare akan sojojin gwamnati a yankuna 13 daga cikin 34 da ake da su, wanda ya hallaka soji 2.

A ranar 10 ga watan nan ake saran kungiyar ta fara tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin Afghanistan bayan yarjejeniyar da ta kulla da Amurka a makon jiya.

Yarjejeniyar ta kunshi ganin Taliban ta saki fursunonin yaki 1,000 da take tsare da su, yayin da gwamnati za ta saki mayakan kungiyar kusan 5,000, abin da shugaban kasa Ashraf Ghani yace ba zai amince da shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.