Isa ga babban shafi

Shugaban Rasha ya kama hanyar tazarce har 2036

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya kafa ginshikin da zai bashi damar cigaba da jagorantar kasar bayan karewar wa’adinsa a shekarar 2024, bayan amincewa da shirinsa na yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, da ‘yan majalisar wakilai suka yi.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin Sputnik/Alexei Nikolsky/Kremlin via REUTERS
Talla

‘Yan majalisar wakilan Rasha 382 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudurin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar ba tare da fuskantar hamayya ba, sai dai 44 sun kauracewa zaman.

Jim kadan bayan samun wannan nasara ce shugaba Putin ya shaidawa ‘yan majalisar wakilan cewa an kama hanyar sauya tsarin shugabancin Rasha, abinda zai bashi damar cigaba da shugabantar kasar har zuwa shekarar 2036, bayan karewar wa’adinsa na karshe na shekaru 6 a 2024.

A Laraban nan majalisar Rashan za ta yi karatun karshe kan kudurin, daga nan kuma ta mikawa majalisar koli ta kasar don neman amincewarta, sai kuma gudanar da zaben raba gardama kan sauye-sauyen kundin tsarin mulkin da zai gudana a ranar 22 ga watan Afrilu dake tafe.

A watan Janairun da ya gabata Putin ya sanar shirinsa na yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, sauyin yanayin siyasa irinsa na farko da rasha ta taba gani bayan na shekarar 1993.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.