Isa ga babban shafi
India

Rububin kwankwadar barasa ya haifar da cinkoso a sassan India

‘Yan Sanda a kasar India sun yi amfani da kulakai wajen tarwatsa tarin mutanen da suka mamaye wani gidan giya, domin kashe kishin da suke da shi bayan kwashe kwanaki 40 a gidajensu ba tare kwankwadar barasar ba.

Jami'an 'Yan Sandan India, yayin kokarin hana mutane karya dokar takaita cinkoson jama'a, yayin da suke kan layin sayen barasa, a Kolkata. 4/5/2020.
Jami'an 'Yan Sandan India, yayin kokarin hana mutane karya dokar takaita cinkoson jama'a, yayin da suke kan layin sayen barasa, a Kolkata. 4/5/2020. AFP
Talla

Rahotanni sun ce sakin marar da gwamnati ta yiwa jama’a daga ranar litinin bayan kawo karshen zaman gidan, ya sa mutane sun yi ta tururuwa inda aka samu tirmitsitsi a Ghaziabad dake Jihar Uttar Pradesh, saboda yadda wasu masu bukatar barasar suka dinga tsallake layi suna zuwa gaba.

Cinikin barasa na daya daga cikin hanyoyin da India ke samun kudaden shiga sosai saboda bukatar sa ga al’ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.