Isa ga babban shafi

India taki amincewa jami'an Amurka shiga kasar

Gwamnatin India taki amincewa ta baiwa Hukumar dake kula da ‘yancin addini na Amurka bizar shiga kasar domin gudanar da bincike kan zargin da ake yiwa hukumomin kasar na cin zarafin mabiya wasu addinai.

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na India Narendra Modi
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na India Narendra Modi REUTERS/Al Drago
Talla

Tun bayan hawar sa karagar mulki a shekarar 2014, Firaminista Narendra Modi na fuskantar zargin yadda ake kaiwa Musulmi hari abinda ya sa wannan hukuma ta Amurka ta bukaci sanya sunan India a matsayin jerin kasashen dake cin zarfin mabiya wani addini daban da kuma sanya takunkumi kan wasu jami’an gwamnatin kasar.

Ministan harkokin wajen India Subrahmanyam Jaishankar ya yi watsi da hukumar ta Amurka wadda ya bayyana ta a matsayin wadda bata san ‘yancin da Yan kasar ke da shi ba.

Ministan ya shaidawa Majalisar Dokokin kasar cewar sun ki amincewa da bukatar baiwa wakilan Hukumar bizar ziyarar kasar da suka bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.