Isa ga babban shafi
India

Tsawa ta hallaka mutum 147 cikin kwanaki 10 a India

Akalla mutane 147 aka tabbatar da tsawa ta yi sanadin mutuwarsu cikin kwanaki 10 da suka gabata can a jihar Bihar da ke arewacin India dai dai lokacin da masana yanayi ke alakanta lamarin da dumamar yanayi tare da gargadi kan yiwuwar fuskantar wasu karin ibtila’in nan gaba kadan.

Daga shekarar 2018 zuwa yanzu, kimanin mutum dubu 2 da 300 tsawa ta hallaka a kasar ta India.
Daga shekarar 2018 zuwa yanzu, kimanin mutum dubu 2 da 300 tsawa ta hallaka a kasar ta India. AFP/Valery Hache
Talla

Ma’aikatar kula da yanayi a India da ke alakanta ibtila’in da sauyi ko kuma dumamar yanayi, ta yi hasashen fuskantar wasu karin bala’o’in da suka zarta wanda ake gani a sassan kasar, ciki har da karfafan tsawa nan da sao’I 48.

A bangaren ma’aikatar kula da bal’o’I ta india ta fitar da kididdigar da ke nuna yadda tsawar ta hallaka kimanin mutum 215 daga karshen watan Maris zuwa yanzu, ciki kuwa har da mutum 147 da ta hallaka cikin kwanaki 10 a jihar ta Bihar.

Da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, Lakshmeshwar Rai ministan bal’o’I a Bihar ya ce bincikensu kan karuwar tsawar da ake fuskanta a wannan damuna ya nuna musu cewa lamarin na da nasaba da tsananin zafin da jihar ke fuskanta wanda ke da alaka ta kaitsaye da dumamar yanayi, yana mai cewa ko a asabar din nan sai da tsawar ta kashe mutum 25.

Yawaitar tsawa tsakanin watan Yuni zuwa Satumba dai ba sabon abu ba ne a India, sai dai a baya-bayan nan ne ta ke halaka tarin jama’a, inda ko a bara ta kashe mutum 170, yayinda ake da jumullar mutum dubu 2 da 300 da tsawar ta halaka daga 2018 zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.