Isa ga babban shafi
Hadaddiyar Daular Larabawa

Karon farko Larabawa sun harba Kumbo zuwa Duniyar Mars

A karon farko wata kasa daga yankin Larabawa ta aike da kumbonta zuwa duniyar Mars wanda aka harba da sanyin safiyar yau Litinin ta sararin samaniyar Kasar Japan.

Lokacin da kumbon Al-Amal ke tafiya duniyar Mars.
Lokacin da kumbon Al-Amal ke tafiya duniyar Mars. Ahmed Jadallah/Reyters
Talla

Da misalin karfe 6:58 na safiyar yau ne aka harba kumbon ta cibiyar harba tauraron dan adam din Japan Tanegashima, wanda ke dauke da bayanan hadaddiyar daular larabawa zuwa duniyar Mars.

Kumbon wanda aka yiwa lakabi da Al-Amal da harshen larabci sau biyu ana dakatar da harba shi saboda gurbatar yanayi amma kuma bayanai sun nuna cewa a yau litinin anyi nasarar harba shi cikin nasara.

Wani bidiyo da kamfanonin labarai suka samu ya nuno yadda wasu wakilan kasar ta hadaddiyar daular larabawa da wasu tsirarun ‘yan Japan a cikin dakin ikon harba kumbon ke murnar nasarar tafiyarsa sa’a guda bayan har ba shi.

Can a birnin Dubai ma, daruruwan al’umma ne suka gudanar da murnar nasarar harba kumbon a ginin Burj Khalifa wanda ke matsayinsa irinsa na farko da wata kasa a yankin larabawa ta harba, inda Sheikh Mohammed bin Rashid Al-Maktoum ke bayyana matakin da gagarumar nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.