Isa ga babban shafi
Afghanistan

Miyagun fursunoni sun tsere bayan harin IS a Afghanistan

Akalla mutane 24 sun rasa rayukansu sakamakon artabun da mayakan IS suka yi da jami’an tsaron Afghanistan a wani gidan yari da ke yankin gabashin birnin Jalalabad, yayin da farmakin ‘yan ta’addar ya bai wa daruruwan fursunoni damar tserewa.

Jami'an tsaron Afghanistan sun farauto kimanin fursunoni dubu 1 bayan sun tsere a artabun da aka yi tsakanin jami'an tsaron da mayakan IS
Jami'an tsaron Afghanistan sun farauto kimanin fursunoni dubu 1 bayan sun tsere a artabun da aka yi tsakanin jami'an tsaron da mayakan IS Reuters/路透社
Talla

A yammacin jiya Lahadi aka fara kaddamar da farmakin, inda mayakan suka bude wuta kan jami’an tsaron bayan sun yi amfani da wata mota makare da bama-bamai wajen fasa kofar shiga gidan yarin Jalalabad.

Wani dan majalisa a lardin Nangarhar, Sohrab Qaderi ya bayyana cewa, kimanin ‘yan ta’adda 30 ne suka kai harin a gidan yarin mai dauke da fursunoni dubu akalla 2.

Kawo yanzu jumullar mutane 24 aka tabbatar da mutuwarsu a harin da suka hada da ‘yan ta’adda uku da fararen hula da kuma jami’an tsaro. Sannan kimanin 43 sun jikkata kamar yadda gwamnatin lardin Nangarhar ta bayyana.

Duk da wannan artabu na bagatatan, jami’an ‘yan sandan Afghanistan sun yi kokarin karkata akalarsu wajen farauto fursunoni akalla dubu 1 daga cikin jumullar fursunonin da suka tsere.

Wannan gidan yarin na Jalalabad na dauke da gaggan mayakan IS da na Taliban da kuma wasu miyagun mutane.

An kai harin ne a daidai lokacin da birnin na Jalalabad ke karkashin dokar kulle domin hana yaduwar cutar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.