Isa ga babban shafi
Lebanon

Tagwayen fashe-fashe sun halaka sama da mutane 100 a Beirut

Firaministan Lebanon ya ayyana zaman makoki sakamakon mutuwar sama da mutane 100 biyo bayan wasu tagwayen fashe-fashe masu karfi da suka auku a birnin Beirut, lamarin da yayi sanadin rusa dimbin gine-ginen da suka danne jama'a.

Daya daga cikin bangarorin birnin Beirut da tagwayen fashe-fashe suka ragargaza.
Daya daga cikin bangarorin birnin Beirut da tagwayen fashe-fashe suka ragargaza. REUTERS/Mohamed Azakir
Talla

Bayanai sun ce an jiyo karfin tagwayen fashe-fashen a nisan kilomita 200 cikin kasar Cyprus da kuma kasar Jordan masu makwabtaka da Lebanon.

Jim kadan da aukuwar wannan iftila’in, Firaministan Lebanon, Hasan Diab ya ayyana zaman makoki, yayin da shugaban kasar, Michel Aoun ya kira taron gaggawa da majalisar tsaron kasar.

Kawo yanzu jami'an agaji sun ce kusan mutane dubu 4 ne suka jikkata sakamakon tagwayen fashe-fashen.

Rahotanni sun ce, mai yiwuwa wasu sinadarai ne da jami’an tsaro suka kama a shekarun baya dake ajiye a rumbunan tashar ruwan birnin Beirut suka haddasa fashewar.

Shugaban rundunar tsaron kasar Abbas Ibrahim ya ce, bisa dukkan alamu, akwai gidan ajiyar karikitai da ke dauke da abubuwan fashewa da jami’an tsaro suka kwace a shekarun baya.

Hotunan bidiyo sun nuna yadda curin bakin hayaki mai kauri ke turnuke sararin samaniya, inda kuma dimbin mutane suka makale a karkashin gine-ginen da fashewar ta ruguza.

Har yanzu dai motocin daukar marasa lafiya na ci gaba da kwashe dimbin gawarwakin mutanen da suka rasa rayukansu a ifltila’in.

Tuni kasar Isra’ila ta fito ta bayyana cewa, babu hannunta a cikin wannan al’amari mai tayar da hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.