Isa ga babban shafi

Zaftarewar kasa ta hallaka mutane 43 a India

A kalla gawakin mutane 43 aka gano a kasar India, bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ta haifar da mummunar ambaliya ta kuma zaizayan kasa, wanda ta mamaye gonakin shayi a kudu maso yammacin Indiya.

Zaftarewar kasa a wani yankin kasar China
Zaftarewar kasa a wani yankin kasar China AFP
Talla

Shugaban ‘yan sandan gundumar Idukki, yankin na lamarin ya auku, Karuppasamy, yace lamarin ya wakana ne tun ranar jumma’a, kuma akasari wadanda iftil’an ya riska ma’aikatan gonan shayin ne.

A daren jumma’a dai gawawwakin mutane 18 a ka gano, kafin adadin ya karu zuwa 43 da maraicen yau Lahadi, sai dai wasu Kafofin yada labaran Yankin sun ce mutane 78 suka bata.

Mutane sama da 300 suka mutu sakamakon ambaliya da zabtarewar kasa a gabashi da arewa maso gabashin India a makowannin da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.