Isa ga babban shafi

An gudanar da zanga-zangar lumana a Iraki

An yi arrangama tsakanin jami’an tsaron Iraqi da masu zanga-zanga a birnin Bagadaza, yayin da suke fita kan tituna don bikin cika shekara 1 da zagayowar ranar da suka kaddamar da boren neman sauyin gwamnatin kasar.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Iraki
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Iraki REUTERS/Thaier Al-Sudani
Talla

Zanga-zangar dai ta gudana cikin lumana a biranen Basra, Najaf da kuma Nasiriyah, sabanin Bagadaza, inda dubban mutane da suka fantsama kan titunan babban birnin kasar ta Iraqi a ranar Lahadi, wadanda suka yi ta daga hotunan daruruwan masu zanga-zangar da suka mutu a shekarar bara.

Masu zanga-zangar sun yi ta jifan ‘yan sanda da duwatsu da zummar yi musu rotse, yayin da su kuma jami’an tsaron suka maida martani da hayaki mai sa hawaye da feshin ruwa, gami da tare wani gungun masu zanga-zangar da suka yi yunkurin kutsawa yankin da aka killace gine-ginen da suka hada da manyan ofisoshin gwamnati, zauren majalisar kasar ta Iraqi, da kuma ofishin jakadancin Amurka.

Majiyoyi daga hukumomin ‘yan sanda da na lafiya sun ce akalla jami’an tsaro 50 ne suka jikkata yayin arrangama da masu zanga-zangar a jiya kadai.

kungiyoyin fararen hula dai sun nuna cewar kimanin mutane 600 suka rasa rayukansu, wasu akalla dubu 30 kuma suka jikkata, dalilin arrangama tsakaninsu da jami’an tsaro, tun bayan soma zanga-zangar neman sauyin gwamnatin ta Iraqi a watan Oktoban shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.