Isa ga babban shafi
Qatar

Kasashen Gulf za su gana don sasanta rikicin Qatar da Saudiya

Kasar Kuwait ta sanar da cewar kasashen dake yankin tekun Fasha za su gudanar da wani taro ranar 5 ga watan Janairu a Saudi Arabia wanda ake sa ran zai sasanta rikicin dake tsakanin Qatar da kasar ta Saudiya.

Wasu gine-gine dake gabar ruwa a Doha, babban birnin kasar Qatar.
Wasu gine-gine dake gabar ruwa a Doha, babban birnin kasar Qatar. REUTERS/Stringer
Talla

Ministan harkokin wajen Qatar Ahmed Naseer al-Mohammed Al-Sabah ya ce taron na da muhimmanci matuka, inda kuma ya bayyana fatan shawo kan matsalolin dake gabansu.

Kasar Saudi Arabia ce dai ta jagoranci kawayenta irinsu Daular Larabawa da Bahrain da Masar wajen katse hulda da Qatar wadda suka zarga da taimakawa ayyukan ta’addanci.

Daga bisani ne kuma suka gindayawa kasar sharadodi 13 da suke bukatar ta aiwatar kafin dawo da hulda da ita, ciki harda rufe tashar labarai ta Aljazeera.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.