Isa ga babban shafi

'Yan Iraqi sun yi boren adawa da karya darajar kudin kasar

Dubban ‘yan Iraqi sun gudanar da zanga-zanga a sassan biranen kasar domin nuna adawa da matakin gwamnati na karya darajar kudin kasar na Dinar da kashi 1 bisa 5 kan Dalar Amurka.

Mutanen Iraqi na zanga-zangar adawa da karya darajar kudin kasar.
Mutanen Iraqi na zanga-zangar adawa da karya darajar kudin kasar. REUTERS/Thaier Al-Sudani
Talla

Matakin rage karfin kudin Iraqin dai shi ne irinsa na farko a tsawon shekaru 50, wanda kuma ya zo a daidai lokacin da kamar sauran kasashe, Iraqin ke fafutukar farfado da tattalin arzikinta da annobar coronavirus ta tagayyara, baya ga yakin da ya  jefa al’ummar kasar cikin kangi.

Kididdiga ta nuna cewar mafi akasarin ‘yan kasar ta Iraqi da suka fita zanga-zangar ta adawa da rage karfin kudin nasu na Dinar dattijai ne, wadanda suka ce matakin ya zaftare darajar kudadensu na fansho.

‘Yan sandan kwantar da tarzoma dai sun kasance cikin shirin ko ta kwana musamman a katafaren filin taro na Tahrir, sai dai zanga-zangar ta gudana cikin lumana.

A baya-bayan nan gwamnatin Iraqi da ta dogara da kashi 90 kan man fetur wajen samun kudaden shiga ta ce, tattalin arzikinta ya durkushe da kashi 11, yayin da a gefe guda Asusun Bada Lamuni na duniya IMF ya ce akalla kashi 40 na yawan al’ummar kasar da ya kai miliyan 40 na cikin kangin talauci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.