Isa ga babban shafi
Saudiya - Qatar

Kasashen Larabawa sun kulla yarjejeniyar hadin-kai da Qatar

Shugabannin Kasashen Yankin Gulf sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin-kai da zaman lafiya bayan jagororin Saudiya da Qatar sun rungumi juna a bainal jama’a, lamarin da ya kawo karshen tankiyar shekaru uku tsakanin Doha da gwamnatocin kasashen Larabawa.

Lokacin da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani ke sanya hannu kan yarjejeniyar hadin-kai da kasashen Larabawa a Saudiya.
Lokacin da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani ke sanya hannu kan yarjejeniyar hadin-kai da kasashen Larabawa a Saudiya. Reuters
Talla

A cikin watan Yunin 2017 ne, Saudiya ta jagoranci hadakar wasu kasashe da suka hada da na Gulf domin katse alaka da zirga-zirgar ababawan hawa tsakaninsu da Qatar wadda suka zarga da dasawar kut-da-kut da Iran, yayin da kuma suka ce tana goyon bayan kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin Islama, zargin da tuni Doha ta musanta.

A yanzu haka dai, wadannan kasashe sun sanya hannu kan yarjejeniyar maido da dasawa a birnin Al-Ula na Saudiya bayan mahukuntan Riyadh sun sake bude kan iyakokinsu na kasa da na ruwa da kuma na sama ga Qatar.

A yayin gabatar da jawabinsa, Yarima mai jiran gadon Saudiya, Mohd. Bin Salman ya bayyana cewa, akwai bukatar gaggauta hada karfi da karfe domin ci gaban yankin Gulf tare da tunkarar kalubale iri-iri da suka hada da barazanar da ke kunno kai daga nukliyar Iran da kuma shirin kasar na yin zagon-kasa ga yankin Gulf a cewarsa.

Kodayake kawo yanzu ba a fitar da cikakkun bayanai kan abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa ba, yayin da masharhanta ke cewa, ba lallai bane duk wata yarjejeniya da suka cimma ta yi gaggawar warware tsauraran matakan da aka dauka kan Qatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.