Isa ga babban shafi

Kotun China da yankewa wani tsohon ma'aikacin Banki hukuncin kisa

Wata Kotu a kasar China ta yanke hukuncin kisa kan wani tsohon Shugaban wata maaikata saboda neman na goro da kuma neman aure alhani kuma yana da mata.

Kotun China ta yanke wa wani tsohon ma'aikacin Banki hukuncin kisa
Kotun China ta yanke wa wani tsohon ma'aikacin Banki hukuncin kisa HANDOUT /Shenyang Municipal Intermediate People's Court / AFP
Talla

Shi dai Lai Xlaomin, wanda kuma tsohon dan jamiyar Communist ne, nunawa tashar TV ta kasar tulin akwatunan kudade da aka cika da takardun kudade a gidansa dake birnin Beijing

A na zargin cewa kudaden da ya mallaka ba da guminsa ne ba, kamar dai yadda aka shaidawa kotun yankin Tianjin.

Bazyaga samunsa da makudan kudade, ana kuma zargin Lai Xlaomin da tuntubar wata mace da yi mata tayin zai aureta, inda har ya yarda ya haihu da maccen, alhani yana da macen aure a gida, sabanin dokokin kasar.

An shaidawa kotun cewa ya nuna tsaban hadamar abin duniya.

Tun a shekara ta 2018 aka dakatar dashi a matsayin shugaban maaikatar tattara kudaden gwamnati, kuma aka kore shi daga jamiyar dake mulkin kasar.

A nashi basin ya bayyana cewa kudade da suka kai $250m, da aka samu a hannunsa yana ajiye dasu ne, amman bai salwantar ba.

Kotun ta ce zaa kwace dukkan kaddarorin da ya mallaka

Tun hawan shugaban kasar Xi Jinping an daure manyan jamiai da dama, amman mutun daya ne rak aka kasha saboda rashawa da almubazzaranci da kudin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.